*🕊️ Tarihin Yaƙin Basasa na Najeriya (1967–1970) 🕊️*
Wannan yaƙin ya faru ne bayan yankin gabashin Najeriya (Biafra) ƙarƙashin *Lt. Colonel Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu* ya ayyana ‘yancin kai daga Najeriya a ranar *30 ga Mayu, 1967*.
Gwamnatin tarayya ƙarƙashin *Janar Yakubu Gowon* ta ƙi amincewa da ballewar, hakan ya janyo *faɗa tsakanin Biafra da Najeriya*.
▶️ *Dalilan Yaƙin sun haɗa da:*
– Rikicin siyasa da kabilanci
– Kashe-kashen ‘yan kabilar Ibo a arewa
– Rabon arziki da iko
– Korar Ibo daga wasu sassan Najeriya
▶️ Yaƙin ya kwashe *shekara uku* (1967-1970) kuma ya haifar da:
– Mutuwar mutane sama da *miliyan daya* (da dama cikin yunwa)
– Halaka da rushewar gidaje da tituna
– Rauni a zaman lafiya da haɗin kan ƙasa
▶️ An kawo ƙarshen yaƙin a ranar *15 ga Janairu, 1970*, bayan Biafra ta mika wuya ga gwamnatin Najeriya.
*Tambaya:*
Shin Najeriya ta koyi darasi daga wannan yaƙin?
*Muhadu a comment👇🏾*
#YakinBasasa #TarihinNajeriya #BiafraWar #GowonDaOjukwu #DarasinTarihi #OneNigeria
