Tashin Hankali: Ma’aikatar tsaro ita kanta bata tsira ba, inda masu garkuwa da mutane suka sace mata Ma’aikata har guda shida.
Kamar yadda zaku gani acikin wannan bidiyon:
Rikicin tsaro ya sake daukar sabon salo a Najeriya, yayin da rahoton Sahara Reporters ya tabbatar cewa ’yan bindiga sun yi garkuwa da manyan daraktoci guda shida daga Ma’aikatar Tsaro (Ministry of Defence) a kan hanyar Kabba–Lokoja, kamar yadda zaku gani acikin wannan bidiyon:
Rahoton ya ce jami’an gwamnatin mata ne gabaɗaya, waɗanda ke kan hanyarsu daga Lagos zuwa Abuja domin halartar jarrabawar karin matsayi. Sai dai a tsakiyar hanya aka dauke su cikin wani shirin harin da aka tsara sosai kamar yadda zaku gani acikin wannan bidiyon:
Msu garkuwan sun tuntubi iyalan waɗanda aka sace, inda suka nemi fansa mai tarin yawa na kimanin naira milyan150,000,000 kafin sakin su. Wannan adadi ya jefa iyalansu cikin ruɗani da tashin hankali, ganin cewa babu wani karfin da zasu iya biyan makamancin wannan kuɗi, kamar yadda zaku gani acikin wannan bidiyon:
Kungiyar ma’aikata ta ASCSN ta bayyana cewa suna cikin damuwar gaske, tana kuma kira da a dauki matakin gaggawa domin ceto rayukan waɗannan jami’an gwamnati kamar yadda zaku gani acikin wannan bidiyon:
Lamarin ya kara nuna yadda rashin tsaro ya kai matakin da har manyan ma’aikatan Ma’aikatar Tsaro ma ba su tsira daga hare-haren ’yan bindiga a hanyoyin kasar ba kamar yadda zaku gani acikin wannan bidiyon:
Har yanzu ana ci gaba da bincike, kuma al’umma na kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki matakan gaggawa domin ganin an dawo da waɗanda aka sace cikin koshin lafiya.
Shin me zaku iya cewa Akan Hakan?
