JIYA BA YAU BA…
A shekarar 1993, Abacha ya rushe tsohuwar Armed Forces Ruling Council (AFRC) lokacin da ya karɓi mulki, ya maye gurbinta da Provisional Ruling Council (PRC), wanda ya zama babban kwamitin yanke shawara na mulkinsa.
Mambobin Kwamitin Mulkin Soja na wucin-gadi (PRC) na Abacha sun haɗa da:
1. Janar Sani Abacha
Shugaban Ƙasa, Kwamanda-in-Chief na Sojojin Najeriya, kuma Shugaban PRC
Ya riƙe cikakken ikon gwamnati da rundunar soji, yana jagorantar dukkan zaman kwamitin.
—
2. Laftanar Janar Donaldson Oladipo Diya
Chief of General Staff kuma Mataimakin Shugaban PRC
Diya shi ne na biyu a mulki bayan Abacha har zuwa lokacin da aka kama shi a 1997 saboda zargin yunƙurin juyin mulki
—
3. Laftanar Janar Ishaya Bamaiyi
Chief of Army Staff
Ya zama Babban jigo a harkokin tsaron gwamnatin, musamman bayan kama Janar Oladipo Diya.
—
4. Vice Admiral Allison Amaechina Madueke
Chief of Naval Staff
Ya wakilci Rundunar Sojin Ruwa a kwamitin kuma ya kula da ayyukan ruwa da gyare-gyare yanda yakamata.
—
5. Air Marshal Nsikak Eduok
Chief of Air Staff
Ya jagoranci rundunar sama kuma ya wakilci Air Force cikin PRC.
6. Laftanar Janar Jeremiah Useni
Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT)
Tsohon abokin Abacha ne na dogon lokaci, kuma ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun muryoyi a siyasar kwamitin.
—
7. Major Janar Abdullahi Sarki Mukhtar
National Security Adviser
Ya jagoranci harkokin leken asiri da tsaro, kuma yana daga cikin manyan masu tsara dabarun mulkin Abacha.
—
8. Alhaji Gambo Jimeta
Inspector General of Police
Ya kula da ayyukan ’yan sanda da tsaron cikin gida har zuwa lokacin ritayarsa a lokacin mulkin.
—
9. Laftanar Janar Mohammed Buba Marwa
Kantoman Mulkin Jiha (Gwamnan Borno, daga baya Legas)
Duk da kasancewarsa gwamna, daga baya an ɗaga mukaminsa zuwa kusa da zoben cikin PRC saboda kyakkyawan aikinsa a Lega
10. Colonel Mohammed Sambo Dasuki
Aide-de-Camp (ADC) ga Abacha / Haɗin kan Leken Asiri
Ba koyaushe yake a matsayin cikakken memba ba, amma yana halartar muhimman taruka kuma yana zama hanyar sadarwa tsakanin Abacha da hukumomin leken asiri.
11. Major Janar Patrick Aziza
Ministan Sadarwa, daga baya Ministan Bayanai
Ya taka muhimmiyar rawa wajen kare manufofin gwamnati kuma ya jagoranci shirye-shiryen yaɗa manufofin mulkin su.
—12. Major Janar John Shagaya
Kwamandan Fage / Manyan mukamai na ma’aikatu
Shagaya, ya yi aiki a fannoni daban-daban kuma ya halarci tattaunawar PRC musamman a shekarun farko
—
13. Brigadier Janar Ibrahim Dabo
Principal Staff Officer ga Abacha
Shine kuma yake da alhakin kula da daidaita dabaru tsakanin fadar shugaban kasa da manyan hafsoshin rundunar soji.
14. Laftanar Janar Mohammed Inuwa Wushishi
Babban Mashawarcin Soja
Ya kasance tsohon jami’in shawara kuma yana shiga zaman PRC lokaci zuwa lokaci.
