A wani yanayi mai kama da juyin mulki, wasu mutane ɗauke da makamai sun kama shugaban ƙasar Guinea Bissau mai ci Umaro Sissoco kwana uku bayan zaɓe, shugaban da jagoran adawa Fernando Dias suka ce su suka yi nasara.
Majiya sun shaida wa BBC cewa sun ji harbe-harbe, kuma wata ta shaida cewa ba ta samu damar fita daga gidanta da ke kusa da fadar shugaban ƙasar ba
