TIRKASHI…
Bayan Shafe Sama Da Shekaru 60 A Legas, An Mayar Da Dattijon Wajen Danginsa A Jihar Kano
A makon jiya ne wasu matasa suka mayar da wannan dattijo gida cikin danginsa a ƙauyen Birgi na ƙaramar hukumar Madobi dake jihar Kano, bayan ya shafe sama da shekaru 60 a Legas.
A rahotannin da muka samu dattijon ya bar gida ne tun yana matashi da ƙarfinsa, amma ya wayi gari ya tsufa kuma yana mararin komawa wajen ‘yan uwansa.
