Close Menu
  • Home
  • News
  • Bollywood
  • Entertainment
  • General sports
    • Basketball
    • Boxing
    • Football
    • Hand ball
    • Race
  • Kannywood
  • Traditional sports
    • Dambe
    • Kokowa
    • Langa
    • Shadi
  • HAUSA
    • Labarai
    • Labari
Latest Posts

JIHAR DA TAFI KOWACE JIHA SAMIN RUWAN SAMA A NAJERIYA 🔥

December 9, 2025

JIHAR DA TAFI KOWACE JIHA NOMA MASARA A NAJERIYA 🔥 

December 9, 2025

JIHAR DA TAFI KOWACE JIHA NOMA FARIN WAKE A NAGERIYA

December 9, 2025
Facebook X (Twitter) Instagram
Facebook X (Twitter) Instagram
PULSE SPORTS ENTERTAINMENTPULSE SPORTS ENTERTAINMENT
Advertise With Us
  • Home
  • News

    Burkina Faso’s Council of Ministers has approved a bill to bring back the death penalty for crimes

    December 6, 2025

    The number of countries facing a US travel ban could rise to above 30 as the Trump

    December 6, 2025

    Nigerian pensioners are planning a nationwide naked protest on December 8 to demand

    December 6, 2025

    West African leaders are calling for united action to protect democracy and the rule of law in the

    December 5, 2025

    Tyla did not appear on the Top 50 Most Streamed Artists on Spotify South Africa 🇿🇦 but She is

    December 5, 2025
  • Bollywood

    Love luxury, traveling and blogging? Have a huge Instagram following? Expert at creating amazing

    December 7, 2025

    Manoj Bajpayee brought the whole team together for a fun and relaxed Family Man Season 3

    December 6, 2025

    Cikin Dukiyar da Jarumi Dharmendra da ya bari crores 450 an tabbatar da crores 5 baza ta tafi zuwa ga yaran sa ba domin akwai wani family a Punjabi da za a bawa.

    December 3, 2025

    Maganar da Jarumi Sunil shetty ya fada kwanan nan akan yan South India sun fi so su bawa yan Bollywood dama su fito a mugu shiyasa yadaina

    November 29, 2025

    AMITABH yana karanta Alkur’ani. Shekarun baya Amitabh ya fito ya bayyanawa duniya cewa yana karanta Alkur’ani mai girma domin samun nutsuwa tare da kwanciyar hankali.

    November 29, 2025
  • Entertainment

    I am just working, i dont have money, what is the value of a celebrity that is not rich, if i tell people

    December 6, 2025

    December 6, 2025

    🔥🇿🇦 South African Football Is Heating Up — And Bafana Bafana Are Becoming a Problem  

    December 6, 2025

    Happy 80th Birthday to Unstoppable Helen Mirren!!❤️🎂🍰🎉

    December 5, 2025

    Aunty Success, born Success Samuel Madubuike on July 9, 2013,

    December 5, 2025
  • General sports
    1. Basketball
    2. Boxing
    3. Football
    4. Hand ball
    5. Race
    6. View All

    🚨𝐎𝐅𝐅𝐈𝐂𝐈𝐀𝐋: Raphinha wins 𝐌𝐚𝐧 𝐨𝐟 𝐭𝐡𝐞 𝐌𝐚𝐭𝐜𝐡 Award for Barcelona on his return! 💙❤️🇧🇷

    November 29, 2025

    🚨 *Neymar Ruled Out for the Rest of 2025 After Knee Injury* 🤕🩼

    November 26, 2025

    Ndigbo Senator Uzor Kalu say he Condemns Nnamdi Kanu For Insulting Justice Omotosho Inside

    November 25, 2025

    How can Dr Congo use juju to play Cameroon and win, and nobody catch them? They now tried the

    November 18, 2025

    “Seeing ourselves up there creates excitement, generates a great atmosphere, and is something to be proud of.”

    November 12, 2025

    A decree from Pope Leo’s office firmly rejects the claim that Mary, Jesus’ mother…

    November 8, 2025

    🚨𝐎𝐅𝐅𝐈𝐂𝐈𝐀𝐋: Raphinha wins 𝐌𝐚𝐧 𝐨𝐟 𝐭𝐡𝐞 𝐌𝐚𝐭𝐜𝐡 Award for Barcelona on his return! 💙❤️🇧🇷

    November 29, 2025

    🚨 *Neymar Ruled Out for the Rest of 2025 After Knee Injury* 🤕🩼

    November 26, 2025

    Ndigbo Senator Uzor Kalu say he Condemns Nnamdi Kanu For Insulting Justice Omotosho Inside

    November 25, 2025

    How can Dr Congo use juju to play Cameroon and win, and nobody catch them? They now tried the

    November 18, 2025
  • Kannywood

    Wani Babban Mutum na Nemawa ’Yarsa Mai Shekara 18 Mijin Aure Mai Hankali da Nutsuwa

    November 24, 2025

    KAJI RABO: An nada Jarumi Tijjani Faraga a matsayin sarkin masoya Annabi (SAW) na Kannywood.

    November 24, 2025

    Me ya sa ba a karrama tsoffin jaruman Kannywood – maza da mata – sai sabbin ‘yan mata da suka shigo masana’antar

    November 24, 2025

    TSEGUMI: Shin ko Jarumar Kannywood Ƴar Auta, tasan irin bidiyoyin da ƴarta Maryam Intete ta ke yi

    November 22, 2025

    WANNAN SHINE MARIGAYI MAJOR JAFAR YUSUF ALIYU, WANDA AKAFI SANIN SHI DA “SARKI SOJA”

    November 22, 2025
  • Traditional sports
    1. Dambe
    2. Kokowa
    3. Langa
    4. Shadi
    5. View All

    Barcelona player

    November 8, 2025

    Barcelona player

    November 8, 2025
  • HAUSA
    1. Labarai
    2. Labari
    3. View All

    JIHAR DA TAFI KOWACE JIHA SAMIN RUWAN SAMA A NAJERIYA 🔥

    December 9, 2025

    JIHAR DA TAFI KOWACE JIHA NOMA MASARA A NAJERIYA 🔥 

    December 9, 2025

    JIHAR DA TAFI KOWACE JIHA NOMA FARIN WAKE A NAGERIYA

    December 9, 2025

    JIHOHIN DA SUKAFI YAWAN MOMA GYADA A NAGERIYA

    December 9, 2025

    MAZAN JIYA: Takaitaccen Tarihin Marigayi Alhaji Abdu Fari (AAF) Katsina 1919-2014

    December 8, 2025

    *🕊️ Tarihin Yaƙin Basasa na Najeriya (1967–1970) 🕊️*

    December 8, 2025

    HAUSAWA KANCE YA GAGARI KUNDILA WANENE HARUNA ?

    December 8, 2025

    Aishatu sule rediyo am kano ‘ gidan bello Dandago : itama tadade tana bamu gudumuwa

    December 7, 2025

    JIHAR DA TAFI KOWACE JIHA SAMIN RUWAN SAMA A NAJERIYA 🔥

    December 9, 2025

    JIHAR DA TAFI KOWACE JIHA NOMA MASARA A NAJERIYA 🔥 

    December 9, 2025

    JIHAR DA TAFI KOWACE JIHA NOMA FARIN WAKE A NAGERIYA

    December 9, 2025

    JIHOHIN DA SUKAFI YAWAN MOMA GYADA A NAGERIYA

    December 9, 2025
PULSE SPORTS ENTERTAINMENTPULSE SPORTS ENTERTAINMENT
Home » TARIHIN SARKIN ZAZZAU MUHAMMADU MAKAU – SARKIN ZARIA BAHAUSHE NA ƘARSHE (1804)
HAUSA

TARIHIN SARKIN ZAZZAU MUHAMMADU MAKAU – SARKIN ZARIA BAHAUSHE NA ƘARSHE (1804)

Yusif Saraki MadigawaBy Yusif Saraki MadigawaDecember 2, 2025
Screenshot 20251202 145631~2

TARIHIN SARKIN ZAZZAU MUHAMMADU MAKAU – SARKIN ZARIA BAHAUSHE NA ƘARSHE (1804)

Sarkin Zazzau Muhammadu Makau shi ne Sarkin Zaria na 61, wanda ya yi mulki a shekara ta 1804.
Kirarinsa:

> Jatau mai masu, ɗan Tasallah, Tozalin barkono ba ka masayi.

Muhammadu Makau ɗan Sarkin Zazzau Sheikh Isyaku Jatau ne.
Sunan mahaifiyarsa Tasallah.
Launin fatarsa jan mutum ne, kuma ba dogo ba.

Bisa al’adar gidan sarauta, idan aka haifi yaro a fadar sarki, zai zauna tare da mahaifiyarsa har sai an yi masa kaciya. Daga nan Sarki zai ɗauke shi, ya danka shi hannun ɗaya daga cikin ‘ya’yan Sarki, ko wani ɗan’uwansa, ko kawunsa.

Wanda aka danƙa yaron gare shi, shi ne zai kai shi makarantar Alƙur’ani, ya ba wani muhimmin malami wanda zai koya masa karatun Alƙur’ani mai girma, kuma ya rika sa shi yana yi masa aikace-aikace na gida kamar ɗibar ruwa, tafiye-tafiye, itace, noma, da sauran ayyuka.

Bayan ya sauke Alƙur’ani da wasu litattafai na addini, sai ya koma gidan kawunsa ko ‘yan uwansa, a yi masa aure.
A nan zai koyi rikon doki, sannan ya rika raka maigidan nasa zuwa yaƙi. Daga baya kuma, idan ya nuna jarumta, a ba shi shugabanci.

Karatu da Rayuwar sa

Makau ya samu damar fadada karatun addininsa sosai, domin mahaifinsa Sultan Muhammadu Isyaka Jatau mutum ne da ya yi fice wajen girmama malamai a fadin ƙasar Hausa. Ya yi kyakkyawar mu’amala da sarakunan ƙasar Hausa da malamai.

Lokacin da Yarima Makau ya kai lokacin aure wasu sun ce na farko, wasu kuma sun ce na biyu amma mafi ƙarfi a tarihi shi ne cewa Sarkin Zazzau Sheikh Isyaka Jatau ya nema wa ɗansa Sultan Muhammadu Makau auren Gimbiyar Kano, ‘yar gidan Sarki Muhammadu Alwali II.
An amince da auren, aka ɗaura shi, wanda ya ƙarfafa zumunci tsakanin Zazzau da Kano.

Halaye da Sarauta

Muhammadu Makau mutum ne jarumi, mai tsoron Allah, kuma mai rikon addini.
Ya hau sarauta a shekara ta 1802 a lokacin saura shekara biyu Fulani su fara yaƙi da sarakunan ƙasar Hausa ƙarƙashin jagorancin Usman ɗan Fodiyo a shekarar 1804 .

A lokacinsa ne Sarkin Kano Alwali II (surikinsa) ya zo Zaria, lokacin da Fulani suka kai masa yaƙi a Kano.
Makau ya karɓe shi, ya zaunar da shi tsawon watanni 13.
Lokacin da Alwali ya nemi Makau ya ba shi bataliya domin ya koma Kano, Makau ya ki amincewa saboda a ganin sa rikici ne da malamai kuma bai so ya shiga rikici da malamai saɓo ne, dukda cewa shima Alwali babban malamin addinin Muslunci ne kuma Basarake.

Sai dai Sarkin Kano Alwali II ya yi masa gargadi, yana cewa:

> “Kamar yadda bamu fahimci sarki Yunfa ba lokacin da ya kira mu a Gobir, ya gaya mana shirin Fulani na amfani da rigar addini, haka ku ma har yanzu baku fahimci meke faruwa ba. Ba gyaran addini suke nema ba, mulki suke so. Kamar yadda suka ci amanar Yunfa, suzo kaina, haka zasu ci amanarka.”

Daga nan Alwali ya bar Zaria zuwa Burun Burun, da niyyar kafa Sabuwar Kano, irin yadda Makau daga baya ya kafa Abuja.

Yakin Fulani da Faduwar Zazzau

A cikin shekara ta 1804, Usman ɗan Fodiyo ya soma yaƙi da Sarkin Gobir, wanda shi ne farkon yaƙin da Fulani suka kaddamar a ƙasar Hausa.
Sun shekara shidda (6) suna yaƙi da sarakunan ƙasashen Hausa.

Daga baya Fulani suka kai wa Sarkin Zazzau Muhammadu Makau hari a Masallacin Idi dake bayan garin Zazzau a shekarar 1807.
Ko da yake Makau yana da jama’a masu yawa, bai sami nasara ba, domin Fulani sun mamaye shi ne a filin sallar Idi bai sami damar komawa gari ya shirya ba.

Sai ya bar garin ba tare da shiri ba, ya nufi kudancin masarautar inda yaje ya sake kafa AbuJA su hausawa da kafa gari aka sansu dama. Wannan ne dalilin da yasa mutanen Abuja suke yin sallar Idi a cikin gari, ba a wajen gari ba, saboda tsoron abin da ya faru da Makau.
Sai lokacin da Turawa suka iso ne aka fara yin sallar Idi a bakin ƙofar gari.

Wannan shi ne dalilin da yasa ake sa dogarawa da ‘yan baka su tsaya a gaban Sarki su fuskanci yamma a lokacin sallar Idi don tuna wa da wancan hari.

Hijirar Makau da Kafuwar Suleja ko Abuja

Ko da yake Muhammadu Makau ya bar garin ba da shiri ba, ya tafi da wasu kayan sarauta, har da wukar Zazzau, ya kai su ƙasar Abuja.
A nan ne ya kafa Masarautar Zazzau AbuJA wanda daga baya ta koma Suleja, wacce daga baya ta zama cibiyar al’ummar Zazzau da suka gudu daga mamayar Fulani.

Muhimmancin Tarihinsa

Sarkin Muhammadu Makau ya kasance Sarkin Zaria Bahaushe na ƙarshe, wanda ya nuna jajircewa da kare mutuncin Hausawa a fagen addini da siyasa.
Ya rasa mulki a hannun Fulani lokacin da suka yi masa juyin mulki a filin sallar Idi, amma ya bar tarihi mai daraja ta kafa Sabuwar Masarautar Zazzau Suleja ko Abuja.

Tarihin sa hujja ce da ke nuna cewa Hausawa suna da tsari, addini, da mulki kafin jihadin Fulani.
Duk wanda yake neman fahimtar ainihin tarihin Zazzau da Hausawa kafin jihadi, dole ne ya fahimci rawar da Sultan Muhammadu Makau ya taka a tarihin ƙasar Hausa.

Manazarta (References)

1. M. G. Smith (1960). Government in Zazzau, 1800–1950. Routledge, London.

2. Daily Trust Newspaper (2021). “Zazzau, Abuja, Suleja: Historical Fact and Fallacy (I)” – discusses the migration from Zaria to Abuja/Suleja.

3. Research Guru Journal (Vol. 11, Issue 1). “The Hausa (Habe) of Abuja before the Fulani Jihad.” — mentions Muhammadu Makau being attacked during Eid prayer in Zaria, 1804.

4. Encyclopædia Britannica. Entry: “Zaria – Historical Kingdom and Province, Nigeria.”

5. Journal of Language, Culture and Religion (Vol. 5, Issue 1, 2024). “The Impact of the Jihad on Hausa City-States.”

Tarihin Sarkin Muhammadu Makau ba wai kawai labari ne na faduwar sarauta ba, shaida ce ta tsayin daka, jarumta, da kishin ƙasa.
Daga rushewar Zazzau ya taso ya kafa Sabuwar Zazzau a Abuja (Suleja) — abin da ke nuna cewa tarihin Hausawa bai tsaya daga jihadin fulani ba, sai dai ya tsira cikin sabuwar rayuwa da mulki.

Wannan tarihin na nuna yadda Sarkin Zazzau Muhammadu Makau, Bahaushe na ƙarshe a kujerar Zazzau, ya fuskanci juyin mulki daga hannun Fulani a filin sallar Idi a shekara ta 1804.
Shi ne kuma wanda ya kafa Masarautar Zazzau (Suleja/Abuja), wadda ta zama wata sabuwar cibiya ta Hausawa bayan rushewar Zazzau ta asali.

> Lura:
Akwai wasu da basa son a kawo tarihin ƙasar Hausa kafin jihadi.
Idan aka kawo tarihin Musulunci kafin jihadi, suna mummunan suka.
Amma tarihi ba ya goge gaskiya — domin haka muke gabatar da wannan daga kundin tarihin masarautar Zazzau Abuja/Suleja.

#hausaactivist

Share this:

  • Click to share on Facebook (Opens in new window) Facebook
  • Click to share on X (Opens in new window) X
Share. Facebook Twitter WhatsApp Telegram LinkedIn Email
Yusif Saraki Madigawa
  • Website
  • Facebook
  • X (Twitter)
  • Instagram

Related Posts

JIHAR DA TAFI KOWACE JIHA SAMIN RUWAN SAMA A NAJERIYA 🔥

December 9, 2025

JIHAR DA TAFI KOWACE JIHA NOMA MASARA A NAJERIYA 🔥 

December 9, 2025

JIHAR DA TAFI KOWACE JIHA NOMA FARIN WAKE A NAGERIYA

December 9, 2025

JIHOHIN DA SUKAFI YAWAN MOMA GYADA A NAGERIYA

December 9, 2025
Add A Comment

Leave a ReplyCancel reply

Latest Posts
Advertisement
© 2025 PULSE SPORTS ENTERTAINMENT. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Disclaimer
  • Privacy Policy

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.