DA DUMI-DUMI: Sarkin Nafada Ya Kaddamar Da Sabbin Dokokin Rage Tsadar Aure A Garin
Daga Muhammad Kwairi Waziri
Wakilin Mai Martaba Sarkin Nafada, Alhaji Umaru Muhammad Baraya (Madakin Nafada), dake jihar Gombe, ya gabatar da sabon tsarin rage tsadar aure da kuma magance matsalolin da ke hana sauƙin aure a cikin al’umma. Taron ya gudana ne a Unguwar Madaki, Gundumar Nafada Central Ward, tare da goyon bayan manyan hukumomi, kotun majistare, da jami’an tsaro.
Sabon dokar za ta fara aiki daga shekara ta 2025, inda matasa suka samu gargadi mai tsanani da kada su tsokani ko raina ’yan mata da kalaman “aure yayi arha”. Duk wanda aka kama yana aikata hakan zai fuskanci hukunci.
Wannan mataki na daga cikin kokarin da ake yi don karfafa tarbiyya da inganta zaman lafiya a Nafada da Jihar Gombe baki ɗaya.
