Author: Yusif Saraki Madigawa

Bokan da ya yi ikirarin taimaka wa ‘yan kwallon kafa na kasar Mali samun nasara a gasar AFCON da ke gudana yanzu haka ya shiga hannu bisa zargin zamba, bayan da ya karɓi Yuro 33,500 (fiye da CFA miliyan 22). Hakan ta faru ne bayan rashin nasarar da Mali ta yi, inda a ranar Juma’a aka fitar da ita daga gasar ta cin kofin Afirka. An kama mutumin, mai suna Sinayogo, a Bamako ranar Asabar, inda ake tsare da shi a sashen yaki da laifukan yanar gizo.

Read More

Gwamnatin Amurka ta mika muhimman kayayyakin soji ga Najeriya domin tallafa wa ƙoƙarin da take yi na yaki da matsalolin tsaro. Jaridar Punch ta ce rundunar sojin Amurka da ke kula da kasashen Afirka AFRICOM ce ta bayyana hakan, inda ta ce an mika kayan ga hukumomin Najeriya ne a Abuja. AFRICOM ta ce wannan mataki na nunar da ci-gaba da samar da haɗin gwiwar tsaro tsakanin Amurka da Najeriya.

Read More

“Halin Kuncin Rayuwa Da Talaucin da ake Ciki A Yanzu, Kuna Goyon Bayan Mu Sake Zabar Tinubu A 2027” – Abba G Shugaban Ƙungiyar Matasan Hausa DevelopmentInitiative, Malam Abba Mohammed Ali, ya yi tambaya ga talakawan Najeriya, musamman waɗanda suka tsaya kai da kafa wajen kafa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kan ko ya dace su ci gaba da tallata gwamnatin bayan gazawar cika muhimman alƙawuran da aka yi musu. Abba Mohammed Ali da aka fi Sani da (Abba G) ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa, inda ya nuna damuwarsa kan yadda talakawa ke fama da matsin rayuwa duk…

Read More

TIRKASHI: G-Fresh Na Shirin Dawo Da Tsohuwar Matarsa Maryam, Bayan Jita-Jitar Wani Minista Na Son Aurenta Shugaban ’yan Kwalta rankatakaf na Najeriya, G-Fresh Al-Amin, na shirin dawo da tsohuwar matarsa Maryam (Nicki Minaj) bayan samun rahotannin cewa wani Minista a gwamnatin tarayya na nuna sha’awar aurenta. Rahotanni sun bayyana cewa ministan ya riga ya ba Maryam kyautar mota, tare da kujerar aikin Hajji, kuma ana rade-radin cewa yana shirin aurenta nan ba da jimawa ba. Bayan rabuwar aurensu da G-Fresh, Maryam ta shahara sosai a kafafen sada zumunta, inda ta zama cikakkiyar ’yar Kwalta, lamarin da ya ja hankalin manyan…

Read More

EL-HADJI DIORI COULIBALY BBC Hausa ‘ shima yabamu nishadi da ilmantar damu a fanni sauraren rediyo a shekarun baya *********************************** Yakan labarai dakuma kawo ruhotanni musamman abinda yashafi kasashen sahel ************************************ Sannan yanayin hira da manyan shwagabanin kasa indai sunje kasar amurka ziyara ‘ kokuma manyan mutane ********************************** Allah yakara masa lafiya da Nisan kwana mai anfani amin ‘ Allah ya albarkaci zuri’arsa amin ************************************ Dawanne shirinsa zaku iya tinawa dashi a shekarun baya ‘ a gidan rediyon BBC Hausa ? ************************************ ✍️ Yau Ibrahim Dankama 09-JANUARY-2026 🌍 ************************************* #mutinabaya #viralreelschallenge #radiokaduna #VOAHausa #radiokano #hausagidana #fmkano

Read More

DA DUMI-DUMI: Sarkin Nafada Ya Kaddamar Da Sabbin Dokokin Rage Tsadar Aure A Garin Daga Muhammad Kwairi Waziri Wakilin Mai Martaba Sarkin Nafada, Alhaji Umaru Muhammad Baraya (Madakin Nafada), dake jihar Gombe, ya gabatar da sabon tsarin rage tsadar aure da kuma magance matsalolin da ke hana sauƙin aure a cikin al’umma. Taron ya gudana ne a Unguwar Madaki, Gundumar Nafada Central Ward, tare da goyon bayan manyan hukumomi, kotun majistare, da jami’an tsaro. Sabon dokar za ta fara aiki daga shekara ta 2025, inda matasa suka samu gargadi mai tsanani da kada su tsokani ko raina ’yan mata da…

Read More