TIRƘASHI: Babban Malamin Addinin Musulunci a Jihar Nasarawa Ya Yi Sama da Fadi da Gidan Marayu, Ya Cinye Kuɗin
Wani babban malamin addinin Musulunci a Jihar Nasarawa ya cin amana da almundahana, bayan da ake zargin ya siyar da gidan marayu da aka damƙa masa kulawa a matsayin amana, tare da cinye kuɗaɗen da aka sayar da gidan.
Majiyoyi masu tushe na kusa da lamarin sun bayyana cewa ba wannan ne karo na farko da ake fuskantar irin wannan matsala ba, domin a shekarun baya an taɓa sayar da gidan marayun, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce da zazzafar muhawara a tsakanin al’umma. A wancan lokaci, bayan doguwar fafutuka, an samu nasarar kwato gidan tare da mayar da shi hannun marayun.
Sai dai bayan wannan badakala, rahotanni sun nuna cewa malamin ya sake komawa ya siyar da gidan a karo na biyu, inda ake zargin ya yi sama da faɗi da kuɗaɗen da aka sayar da gidan.
