Bokan da ya yi ikirarin taimaka wa ‘yan kwallon kafa na kasar Mali samun nasara a gasar AFCON da ke gudana yanzu haka ya shiga hannu bisa zargin zamba, bayan da ya karɓi Yuro 33,500 (fiye da CFA miliyan 22). Hakan ta faru ne bayan rashin nasarar da Mali ta yi, inda a ranar Juma’a aka fitar da ita daga gasar ta cin kofin Afirka.
An kama mutumin, mai suna Sinayogo, a Bamako ranar Asabar, inda ake tsare da shi a sashen yaki da laifukan yanar gizo.
