Da alamu Jarumi Ajay Devgan zai yi remake bangaren Hindi na film din Mohanlal me taken ‘Thudarum’ film ne akan wani mutum matukin tasi me suna “Benz” watau Shanmugham wanda yake tare da matar sa da yaran sa guda biyu.
Film ne me kyau wanda ya sha yabo wajen yan kallo da masu sharhi.
Anyi shi da yaren Malayalam a wannan shekarar 2025 kuma yanzu ana shirin yin sa da Hindi idan kome ya daidaita.
