TIRKASHI: G-Fresh Na Shirin Dawo Da Tsohuwar Matarsa Maryam, Bayan Jita-Jitar Wani Minista Na Son Aurenta
Shugaban ’yan Kwalta rankatakaf na Najeriya, G-Fresh Al-Amin, na shirin dawo da tsohuwar matarsa Maryam (Nicki Minaj) bayan samun rahotannin cewa wani Minista a gwamnatin tarayya na nuna sha’awar aurenta.
Rahotanni sun bayyana cewa ministan ya riga ya ba Maryam kyautar mota, tare da kujerar aikin Hajji, kuma ana rade-radin cewa yana shirin aurenta nan ba da jimawa ba.
Bayan rabuwar aurensu da G-Fresh, Maryam ta shahara sosai a kafafen sada zumunta, inda ta zama cikakkiyar ’yar Kwalta, lamarin da ya ja hankalin manyan mutane da dama masu kuɗi da madafun iko, waɗanda suka fara nuna sha’awar zawarcinta.
Majiyoyi na kusa da G-Fresh sun ce wannan ci gaba ne ya sa ya fara tunani da shirin sake dawo da ita, domin kada ya rasa tsohuwar matarsa ga wani babban mutum a gwamnati.
