“Halin Kuncin Rayuwa Da Talaucin da ake Ciki A Yanzu, Kuna Goyon Bayan Mu Sake Zabar Tinubu A 2027” – Abba G
Shugaban Ƙungiyar Matasan Hausa DevelopmentInitiative, Malam Abba Mohammed Ali, ya yi tambaya ga talakawan Najeriya, musamman waɗanda suka tsaya kai da kafa wajen kafa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kan ko ya dace su ci gaba da tallata gwamnatin bayan gazawar cika muhimman alƙawuran da aka yi musu.
Abba Mohammed Ali da aka fi Sani da (Abba G) ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa, inda ya nuna damuwarsa kan yadda talakawa ke fama da matsin rayuwa duk da irin gudunmawar da suka bayar wajen samun nasarar wannan gwamnati a zaɓen 2023.
Ya ce, “Mu ne muka yi wahala, muka yi aiki tukuru domin wannan gwamnati ta hau mulki. Amma zuwa yanzu, da yawa daga cikin alƙawuran da aka yi mana ba a cika su ba. To tambaya ita ce, shin ya dace mu ci gaba da tallata wannan gwamnati ga talakawa?” in ji shi.
Shugaban ƙungiyar ya jaddada cewa talakawa suna jin an watsar da su, musamman ta fuskar tsadar rayuwa, rashin aikin yi, da matsalolin tsaro da ke addabar sassan ƙasar nan.
Ya buƙaci gwamnati da ta saurari kukan jama’a tare da gaggauta ɗaukar matakai masu ma’ana domin rage wahalar da talakawa ke ciki, kafin neman ƙarin goyon baya ko tallata kanta a idon jama’a.
A ƙarshe, Abba Mohammed Ali ya ce ƙungiyarsa ba ta adawa da gwamnati kai tsaye, amma tana neman adalci, gaskiya da cika alƙawura, yana mai jaddada cewa goyon baya na gaskiya sai an ga ayyuka a ƙasa, ba magana kawai ba.
