HAUSAWA KANCE YA GAGARI KUNDILA WANENE HARUNA ?
A fagen kasuwanci a kasar Hausa duk abunda akace ya gagari Kwandila to ba zai siyu ba. Kundila ya yi shaharar da har an samu saka sunayenshi a wasu gine-gine na gwamnati a jahar Kano. Kamar jerin gidajen Kwandila, makarantar firamari ta Kwandila da dai sauransu.
Kundila mutun ne da yai rayuwa irin ta talakawa, domin bayacin abinci mai tsada, baya sa sutura irin ta kawa, duk da dinbin arzikin da Allah ya bashi.
Sunan Mahaifin Kundila Ahmadu Ba’agale. A wani kauli na tarihi ya ce an haifi Haruna Kwandila ne a Gozeye wacce take kusa da Dorayi.
Alhaji Masallaci Magaji wanda ya fito daga cikin tsatson Kundila, yace an haifi Kwandila ne a garin Garko, Kuma anan ya taso. Shi daman garin Garko wurine da akasan shi da Agalawa, kusan sun yi kakagida a garin na Garko. Duk da yake ba’asamu wasu kwarara ko gamsassun bayanai akan tasowan Kundila ba. Amma ance ya taso ne a hannun yayarsa mai suna Gwarya, wacce itama fitacciyar yar kasuwace.
A wanchan lokacin ita Gwarya tana zaunene a Makwarari wacce take cikin Dala. Bayan karatun Allo da ya yi, Kwandila nada shekaru shabiyu ya fara yawon talla, yana siyarda tsakiya da goro, idan ya siyar akan bashi kamasho. Kwandila na yawon talllanne wararen kasuwar Kurmi. A wanchan lokacin bai kai munzalin balagaba, ana ciyar dashi ne kuma anamai sutura. Kwandila ya yi amfani da wannan damar ya rika adana kamashonshi.
A hankali a hankali Kwandila ya fara siye da siyarwa, na wasu kayayyaki cikin su hadda runannun Kaya. Bayan shekaru biyu Kwandila ya bunkasa shima kanfishi ya kawo. Ya farabin ayarin matafiya masu zuwa Gonja. A wanchan lokacin Kwandila bayi da karfin da zai rika dorama dabobi kayanshi. Kwandila ya yanke hukuncin shine zai rika dauko kayanshi a kai tundagatundaga Gonjan har Kano.
Hakan yasa Kundila yafi abokanan kasuwanci shi, cin riba tunda baya dorama dabbobi kayanshi, shi yake daukar abunshi. Bayan wani dan lokaci Kwandila ya yi hayan mutane biyu da zasu rika rakashi Gonja suna dauko mishi kaya akan su.
Ba’a dauki tsawon lokaci ba Kundila ya siya gidansa na harko a unguwar Makwarari, kuma ya yi auren fari. Bayan shekaru goma Kwandila ya zama daya daga cikin manyan attajiran Kano, yama dai na zuwa Gonja. Ya rika bada sautu ta hannun dillalai shima. Kwandila ya zama shahararren attajiri kafin Allah ya karbi rayuwarshi cikin 1902. Yabar “yaya biyar ga sunayensu Ali, Muhammad, Bawa, Hauwa, da Jummai.
