Ka shekara Goma Ko ashirin Kana neman kudi Kawai Don Ka Auri Mace Yar’ Zaman banza , Jahila, Mara Mamora Wadda Kanta Babu Komai sai Jiran duk Sati a saki Sabon Film Hausa series, Gidan sarauta, Jamilun Jidda, Zabi Biyu da duk wata Kwamacala.
A haka zaka gina goben iyalinka Mai kyau kuwa ?
Kana son Ya’yanka su koma Bara idan ka rasu koh? Idan Allah yasa ka rasu da wuri da dan sauran kwarinta dole tayi aure ko don ta samu ta dinga ci tana koshi kai kuma Ya’yanka sai dai a raba su wannan yana kauyen Warawa wajen Kanwar Babansa Naja’atu labule Warawa tana taimaka masa tana bashi abinci.
Dayan Kuma yana can layin makwalla Wajen Kanin babansa Garba shuɗi ya taimaka ya dubi zumunci ya rikeshi yana Jiqa masa kwaki yana masa gori yayinda Ya’yan cikinsa yake labewa yana siya musu kilishi.
Tun daga Zaben Matar Aure Na miji ke rusa rayuwarsa wadda wata rushewar wallahi bazai sake ginata ba har abada, kana dauka cewa kai namiji ne komai zaka iya koh ?
Malam Ka bude idonka ka wangale kunnuwanka kafin ka fara tunanin auren yarinya kayi mata Screening, ka yi Observation, sannan kayi “examining”.
Idan ba haka ba kasake ka mutu Abokanka su Mayar Da ita karuwar gida Duk wanda taje Maula wajensa Neman kudin abincin da Zata Bawa Marayun Ya’yanka Sai sun gama Ɗangaleta” Kamar Keke napep Sannan su siya Mata Rabin kwanon shinkafa da taliya Daya.
Soyayya kawai bata isa ka auri mace don ita ba, Soyayya kawai bata iya rike aure sai an samo mata mataimaka.
Amma ba Nasibi akanka idan kayi shekara da shekaru kana neman kudi kawai don ka auri Macen da bata iya Komai ba, Wannan shine Hannun Dama ya samu na hagu ya watsar.’ 👌
Allah ya kyauta 🙏
Allah kasa mu dace
Fatima Muhammad 💓.
