Marigayiya Dala Isah Bakori : itace Bariki matar Usman baba Fategi acikin shirin Samanja mazan fama ” dakuma ” Duniya budurwar wawa “sune jarumanmu na farko farko wajen wasan kwaikwayo
__________________________________
Dala Isah Bakori sunbamu nishadi a shekarun baya ‘ a lokacin mulkin soja ‘ inda suka nishadantar damu da shirin wasan kwaikwayo mai kayatarwa na Samanja mazan fama ‘ bayan karbar mulkin farar hula ‘ sai aka maida shirin ” Duniya budurwar wawa ”
________________________________
Dala Isah Bakori ‘ ta’iya acting Bariki sosai ‘ a matsayin matar soja mai matsayin Sargent major ‘ Wanda aka chanza sunan daga turanci zuwa Hausa ake cewa “Samanja ” ta’iya magana da pidgin English irin na matan sojoji
______________________________
Bayan rasuwar Dala Isah Bakori ‘ sai aka maye gurbinta da ” Tabature Dandume” itama taci gaba da bamu nishadi ‘ kafin rasuwarta itama tabamu nishadi a wannan shirin na gidan rediyon tarayya Kaduna
______________________________
Abokanin Aikinta acikin shirin Samanja dakuma Duniya budurwar wawa ”
“Usman baba fategi Samanja ”
” Ibrahim Abubakar faskari ”
“Haruna danjuma Mutuwa dole ”
“Kabani kanaka”
“Tabature Dandume ”
“Idon mujiya ”
etc
_______________________________
Dame kuke tinawa dashi a wadannan shirye shiryen ‘ Samanja ‘ dakuma Duniya budurwar wawa ” ?
_________________________________
Allah yajikan ta da rahama ‘ tareda sauran wadanda suka rasu daga cikinsu amin ‘ Allah ya albarkaci zuri’arsu amin ‘ wadanda suke Raye daga cikinsu Allah yakara musu lafiya da yalwar arziki amin
_______________________________
✍️ Yau Ibrahim Dankama
19-November-2025 🌍
_____________________________
www.madigawadatasub.com.ng
