MAZAN JIYA: Takaitaccen Tarihin Marigayi Alhaji Abdu Fari (AAF) Katsina 1919-2014
Daga Dakta Sani Abdu Fari
Asalin Suna Da Shekarar Haihuwa
Marigayi Alhaji Abdu Fari sunansa na yanka Abdullahi kuma sunan mahaifinsa Kafarda Muhammadu Gidado Dan Kusada Muhammadu Bello Dan Bebeji Muhammadu Gidado Dan Sarkin Katsina Malam Umarun Dallaje, Dan Abdulmumin Abubakar (Mummuni), Dan Abubakar Muhammadu (Garba Madambacin Gabas), Dan Muhammadu Magoshi. An haifi marigayi Alhaji Abdu Fari a shekarar 1919 a Unguwar Madawaki cikin garin Katsina. Yayi makarantar koyon karatun Al’qur’ani a makarantar Liman Malam Audi da ke unguwar Liman a garin Katsina.
Takaitaccen Yawon Kasuwanci, Abokan Hudda Da Kuma Iyayen-gidansa
Ya fara kasuwanci tun yana dan shekara goma sha biyar yana daukar goro daga gidan Uwar-dakinsa Hajia Baika (mahaifiyar su Alhaji Raben Baika, Iron Baba da Dahiru Saude), a lokacin Hajiya Baika tana kiranshi da suna ‘Danhamsin Dan’albarka’ marigayin ya kasance yana bin kasuwanni dayawa kaman kasuwar Danmusa, Dutsinma da sauransu. A wannan lokaci ne kuma yake sayen dinkakkun riguna yana sayarwa shida yayansa Marigayi Alhaji Musan Kafarda. Baccin Hajiya Baika kuma marigayin yana da wani maigidan wanda ake kira Alhaji Gani (Mahaifin Alhaji Musa Gani) wanda yake bashi huhunan goro yana sayarwa, a wancan lokacin idan yakai kaya Dutsinma yana zama gidan wani attajiri da ake kira Wowon Labon-Didi yana koyon dinki, bayan wani lokaci likkafar kasuwanci tayi gaba sai ya yi hijira ya koma garin Jos yana dinkin Jikkuna da sauran aikace aikace na sana’arsa, yana nan yana wannan kasuwanci a garin na Jos.
A lokacin zamansa garin Jos jarinsa ya habaka wannan ya sanya ya nemi matsawa gaba domin fadada cinikayya fannin saye da sayerwa, likkafa ta kara gaba inda ya koma garin Ile-Ife na Jihar Oyo a yau, a shekarar 1943 ya kama harkar tankun goro, Allah yayi mashi kwazo da jijircewa ta fuskar kasuwanci da kokarin nema, alokacin sai ya fara sayen huhunan goro yana kawowa a garin Ibadan inda mutanen arewacin Nigeria suke zuwa sari.
Marigayin ya tafi zuwa aikin Hajjinsa na farko tare da mahaifinsa a shekarar 1956 lokacin yana dan shekara 36, a wannan tafiyar ne suka hadu da Ahmadu Bello Sardauna lokacin da suka hau jirgin sama mai cin zango a kasar Khartoum kan hanyarsu ta zuwa kasa mai tsarki.
Ba da jimawaba marigayin yayi fice wajen sana’ar ta goro har ya kasance ya koma a garin Iteku inda shima babbar kasuwace ta saye da sayarwar goro, sanda ya koma garin Iteku ne alokacin ya rika aikowa da huhunan goron zuwa arewacin Nigeria a cikin jirgin kasa har zuwa Funtua, Gusau, Sokoto da Kano. Bayan yan shekaru marigayin ya koma garin Ibadan da zama, zamantakewarsa a wadannan wurare ne ya sanya marigayin ya kware da harshen Yarbanci hatta da Iyalinsa suma suka nakalci yaren na Yarbanci. Yayi Shekaru Ashirin a unguwar Sabo cikin garin Ibadan a inda sukayi zamantakewa da huddodi na arziki da wasu mutanen Arewacin Nigeria.
Wasu daga cikin abokanen huddarsa sun hada da Alhaji Mamman Fari Kano, Alhaji Tanko (Mahaifin Alhaji Labo Tarka), Alhaji Barau Mai Fanka, Alhaji Jibrin na Madugu, Alhaji Ali Bagobiri, Alhaji Sani Mashal, Alhaji Mamman Mai kekune Kano, Alhaji Bako Jagindi, Alhaji Lawal na Kadiri Kura Kano, Alhaji Abdu na Idi Gora, Alhaji Mamman Dan Mai-Teba, Alhaji Dan-Baba Mijin Maigari, Alhaji Mamman Alabura Bamalle, Alhaji Mamman Ifo (Sarkin Yakin Katsina), Alhaji Ubaidu, Alhaji Danlami Na-mai-kalango Ibadan, Alhaji Dauda Kambari, Alhaji Kari Borno, Alhaji Garba Sagadan, Alhaji Mudi dan-Zaki (shugaban jam’iyyar NPC a Ibadan), Alhaji Garba na Bara Dan Sukuwar Dawaki, Alhaji Dikko dan Sarkin Hausawa Ibadan da sauransu Kafin ya dawo gida Katsina a lokacin da fitina tayi yawa sanadiyyar kashe Ahmadu Bello Sardauna.
Dawowa Gida Katsina
Alhaji Abdu Fari ya dawo gida Katsina a cikin shekarar alif da dari tara da sittin da bakwai (1967) a lokacinne ya fadada kasuwancinsa da harkokinsa wanda ya kunshi sufuri tun lokacin ‘MAN DIESEL mai Uwa da Diya’, Marsandi(Mercedes) da Bilhodu(Bedford) wanda alokacin Alhaji Halliru Kafur(Hali Brother) abokinsa kuma amininsa yana Janar Manaja na kanfanin UTC a Kano, sauran sana’o’insa sun hada da kwangila, noma, Kamfanin sayar da kaya(spare parts) na manyan motoci Automotive Parts Industry (API) a Kano da sauran harkoki. Wasu daga cikin manyan kwangilolin da ya farayi sune yin kwangilar magudanan ruwa daga Ajiwa Dam zuwa sassan garin Katsina da kewaye, aikin Dam na Bakori, da Dam din Bakolori, da gidajen Mafara sai kwangilar ginin makarantu masu yawa irin su makarantar sakandare ta Gangara, Ministry of works ta Mani, GGSS Kankiya, WTC Katsina, Fertilizer stores masu yawa a fadin Katsina Kaman na Safana, Dutsinma, Katsina, da dakin koyon aiki (workshop) na makarantar BATC a nan garin Katsina da sauransu.
Alhaji Abdu Fari ya zama fitaccen mai sufuri (transporter) a Afrika da Duniya baki daya wanda za’a iya gani a shafunan yanar gizo yanzu da zaran an rubuta sunansa a GOOGLE wanda har ya zuwa yanzu kanfunnan kerawa da sayar da manyan motoci da injina wadanda yayi hudda dasu na kasashen Germany, Holland, America da England suna aiko da littattafai(catalogue) da wasiku zuwa ga adireshinsa, ya kasance mai sufuri na takin zamani, kayan gona, Shanu da kayan man fetur a duk fadin Nigeria. Marigayin shine shugaba (chairman) na farko na masu sufuri (NARTO) a Katsina, kuma yayi sshugaba na farar hula na hukumar kare hadurra (Road Safety) a Katsina, yayi zama mamba(member) na hadin kan yansanda da mutanan gari (Police Community Relations Committee) a Katsina.
Wasu daga cikin ayyuka da kasuwancinsa a Katsina
Marigayi Alhaji Abdu Fari ya zama babban mai sufuri (transporter) kuma wakili na kamfanin mulmula karafa (Katsina Steel Rolling Mill), babban dealer na gidan simintin Sakkwato (Sokoto Cement), Gidan simintin Ashaka (Ashaka Cement), kamfanin kayan masarufi na Lever Brothers, Kamfanin lemun sha na Brahma Guarana da dai sauransu. Alokacinnan marigayin yayi gine gine masu yawa tare da taimakon addini ta fannoni daban daban wajen gina Islamiyoyi, rijiyoyi da manyan masallatai na jumu’a akarkashin kulawar babban yaronsa kuma amininsa Alhaji Sani Danballaje.
Marigayin ya kasance Dan-majalisar Sarkin Katsina tun bayan nadin marigayi Maimartaba Sarkin Katsina Alhaji Muhammadu Kabir Usman saboda kauna da aminci dake tsakaninsu da Sarki tun da dadewa, wannan kauna ta zarce har ya zuwa Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmummuni Kabir Usman wanda alokacin da Alhaji Abdu Fari ya rasu Sarkin yataso ya taho gidan marigayin ya zauna na tsawon lokaci har akayi masa sutura da salla kuma alokacin Mai Martaba Sarki yake nuna jimamin rashin mutun irin Alhaji Abdu Fari ga masarautarsa da kasar Katsina baki daya. Sannan kuma marigayin ya kasance mamba na Gidauniyar Jihar Katsina tun da aka kafata a karkashin jagorancin Janar Muhammadu Buhari har ya zuwa lokacin da ya rasu.
Bai Wa Ilimi Mahimmaci
Neman ilimi na addini da na zamani wani al’amari ne mai matukar muhimmance a wajen marigayi Alhaji Abdu Fari wanda a lokacin rayuwarsa zakaji yana yawaita fadin “WANDA BASHI DA ILIMI KO A GIDANSU ICCEN DARNI NE, A BAYA YAKE”, hakan ya sanya cewa babu wani abu da yayansa, dangi da masu jibantarsa suka fi samun romon tallafi a wurinsa sama da harkar Ilimi. Ya kasance mai tsare yayansa suna karatun Allo da na littafan addinin musulunci a cikin Gidansa, sannan kuma ya sama wa yayansa guraben neman ilimi a makarantu Kaman su BUK, UDUS, ABU, UNIMAID, Zoom technologies India, Linton University College Malaysia da sauran makarantu a Nigeria da kasashen ketare. Hatta almajirai masu yin hidima a Gidansa suna da kaso na tallafin neman ilimi wanda mafi yawancinsu ya sanya su makarantar ATC a Katsina, sakamakon yin hakan, a yanzu haka akwai kimanin mutum guda a cikin almajiransa wanda yake da PhD, guda hudu suna da Master Degree sannan misalign guda 47 suna da Degree na farko kuma mafi yawancinsu suna aikin koyarwa ko kuma aikin ofisoshi a jihohin Katsina, Zanfara, Kebbi, Sokoto da Jigawa. Wannan ba karamin kokari ba ne tare da hangen nesa da kokarin taimakon al’umma.
Ayyukan Addini
Marigayi Alhaji Abdu Fari ya kasance mai hazaka da kula da addini a duk inda yake kuma yana kokarin taimakawa da inganta lamurra na addinin musulunci ta fannoni daban daban irin su gina Islamiyyoyi da masallatai na hamsu salawatu da kuma na sallar Jumu’a masu yawa a fadin jihar Katsina da wasu wuraren ta hanyar samun labarin bukatuwar yin hakan daga malamai masu da’awa a duk sassan kasar Nigeria da Niger Republic. Wadansu daga cikin malamai da mutanen da suka taimaka wajen yinwadannan ayyuka sun hada da Marigayi Liman Lawal na babbab masallcin Katsina, Malan Abbate, malan Muttaka Unguwar Liman, Malan Sulaiman Dutsin-Amare, Malan Yakubu Musa Hassan, Alhaji Sani Danballaje, da sauransu. Marigayin kuma yana daya daga cikin mutane na farko da suka rika gyaran makabartu da dukiyarsu ciki da wajen Jihar Katsina.
A fannin ruko da addini kuwa marigayin ya zama abun nuni da kuma koyi, saboda harkokinsa na kasuwanci basu hanashi kula da sallolinsa Hamsu salawatu ba a cikin Jam’i kullun kuma a babban masallacin jumu’a na garin Katsina, wanda hakan ya sanya marigayin ya zama tamkar agogon da ke nuna lokacin salla, har ya kasance limamin babban masallcin Katsina yakan bashi ratar mintina kafin ya tada salla idan bai ganshi ba, sanin cewa lallai akwai lalurin da ya dan rikeshi amma yana kan hanyar sa ta zuwa masallacin. Duk sanda Jama’a suka ga ya taho a motarsa to lallai lokacin salla yayi kenan, kullun babu fashi har lokacin da jikinsa ya gaza saboda tsufa da rashin lafiya wanda shi yayi sanadiyyar rasuwarsa.
Rasuwa Da Kuma Wasu Daga Cikin Ƴaƴansa Da Iyalinsa
Marigayi Alhaji Abdu Fari ya rasu a gidansa da ke kan hanyar zuwa Kofar Kwaya Katsina a ranar Laraba 29 ga watan October 2014 yana da shekaru 94 a duniya. Ya bar matansa su hudu (4) da yayansa 43 (Maza 20 da Mata 23) da Jikoki masu yawa. Allah Subuhanahu wata’ala Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa kurakurensa ya sadashi da rahamarSa Ya sanya aljanna ce makomarsa tare da dukkan sauran musulmi baki daya, ameen.
Daga shafin Arewa Jiya Da Yau
