Wane ne sabon sufetan ƴansandan Najeriya Tunji Disu?
Shugaban Najeriya ya sanar da naɗin Olatunji Rilwan Disu a matsayin sufeta-janar na ƴansandan kasar, bayan ajiye aikin tsohon mai riƙe da muƙamin Kayode Egbetokun.
A cikin wata sanarwa da fadar shugaban Najeriya ta fitar, Tinubu ya ce ya amince da ajiye aikin Sufeta-Janar Kayode Egbetokun “bayan ya miƙa takardar ajiye aiki bisa dalilai na iyali”.
Tinubu ya gode wa tsohon sufeta-janar ɗin tare da yaba masa “bisa gomman shekaru da ya kwashe yana hidimta wa rundunar ƴansandan da kuma Najeriya”.
A watan Yunin 2023 ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa Kayode Egbetokun a matsayin sufeta-janar na ƴansandan ƙasar, da sa ran zai yi jagoranci na tsawon shekara huɗu, zuwa watan Yunin 2027.
