WATA SABUWA: A Shari’ance An Fara Bayyana Irin Hukuncin Da Ka Iya Biyo Baya Akan Jami’in Sojan Ruwa Yarima Da Ya Hana Ministan Abuja Nyesom Wike Duba Wani Fili
Fitaccen lauya kuma masanin tsarin mulki Najeriya, Farfesa Sebastine (SAN), ya bayyana cewa jami’in rundunar ruwa, A.M. Yerima, ya karya doka a rikicin da ya faru tsakaninsa da Ministan Babban Birnin Tarayya, Barr. Nyesom Wike, a wani fili da ake gardama a Abuja.
A wata sanarwa da Farfesa ya fitar, ya ce jami’in ya hana Ministan shiga filin ne bisa hujjar “bin umarnin manya,” amma hakan ya sabawa doka da kuma tsarin mulki na ƙasa. Ya yi nuni da cewa Kotun Koli ta Najeriya ta taɓa yanke hukunci cewa babu wani jami’i da zai iya bin umarnin da yake bayyananne haramtacce ko rashin adalci.
Farfesan ya ƙara da cewa babu wata doka da ta amince da jami’in soja ya yi gadin wurin ginin mallakin tsohon shugaban sa, musamman a yanayi da ake zargi da rashin gaskiya wajen mallakan filin, Ya ce idan akwai barazanar ta take haƙƙi, abinda ya dace a hukumance shi ne a kira ’yan sanda na farar hula, ba a tura soja ba.
Ya kuma jaddada cewa, a matsayi na doka, Ministan Abuja na matsayin Gwamnan Jiha ne, kuma shi ne ke da ikon kula da dukkan filaye a Abuja bisa sashe na 297(2) da 302 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.
“A wannan rana, Wike yana tsaye ne a matsayin wakilin shugaban ƙasa da kuma babban kwamandan rundunar soji. Saboda haka, ko da tsohon jami’in ruwan yana aiki ne baiyi ritaya ba, bai da ikon hana Minista Abuja shiga filin,” in ji shi.
Farfesan ya bayyana cewa ko da hanyar da Ministan ya bi tana da ƙarfi, duk abin da ya aikata yana bisa doka. Amma jami’in da ya hana shi ya aikata laifi wanda ya sabawa Dokar Rundunar Soja (Armed Forces Act), wacce ke cewa sojoji na iya fuskantar hukunci idan suka aikata laifin farar hula.
“Jami’in soja ko ɗan sanda na rantsuwa ne wajen kare tsarin mulki, ba wai bin kowanne umarni ba. Idan ya bi umarni da ya sabawa doka, shi ke ɗaukar alhakin aikinsa,” in ji Farfesa.
Ya gargadi cewa rashin hukunta jami’in na iya ƙara haifar da ƙarfin guiwar sojoji su raina fararen hula, su kuma yi ikirarin cewa “mun yi wa Wike haka, babu abin da ya faru.”
Menene ra’ayinku?
