Aisha buhari
Tana daga cikin Diary na baba buhari wadda ta taka muhimmiyar rawa A rayuwarsa
Ta raka shugaban har sau 2 wajen rantsarwa A matsayin lamba 1 ta kuma fuskanci abubuwa dama daga media ganin irin Labaran jita jita Da yan Nigeria suka yada na batun Kara Aure da wata ma’ana za ai mata kishi ya
A lokacin bata kasar daga saukarta a filin jirgin sama BBC Hausa tayi hira da ita ga amsar data bada
Bayan dogon lokaci ba ta kasar har ake jita-jitar ta yi yaji ne, mai dakin Shugaba Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta koma kasar, inda ta sauka a Abuja a cikin daren da ya gabata kuma ta tattauna da manema labarai.
Bayan saukarta a filin jirgin sama na Abuja, Aisha Buhari ta yi watsi da jita-jitar da aka rika bazawa cewa ta yi yaji ne inda ta ce ta tafi ne domin a duba lafiyarta sannan kuma ta samu lokaci da ‘ya’yanta.
Ta yi shagube ga wacce aka ce Buhari zai aura inda ta bayyana wa Awwal Janyau cewa “Ita wadda aka ce za a aura ai ba ta musanta batun auren ba sai da ranar auren ta wuce tukuna ta musanta.” 😂😂😂🙏 wannan ya nuna tana kishin da sahabinta wanda take matukar kauna
Ta ce kwanakin da ta shafe ba ta Najeriya ba ya da alaka da zargin da ake cewa yaji ta yi domin kara armashi ga jita-jitar da ake ta yadawa cewa shugaba Buhari na shirin Kara Aure
Allah ya gafartawa shugaba buhari Aisha buhari tasan Waye mijinta da tsayuwarsa akan ra’ayi🙏
