KUNDIN AIKIN JARIDA (2)
12 GA YUNI: LOKACIN DA NAJERIYA TA SHIGA MUMMUNAN RIKICI
Rahotannin da muka bayar a BBC bayan soke zaben shugaban kasa na ranar 12 ga Yunin 1993, sun nuna yadda Najeriya ta fada cikin daya daga cikin mafi munin rikice-rikicen siyasa tun bayan samun ’yancin kai. A kankanin lokaci, yanayin kasar ya fara sauyawa.
Tambayar da aka dinga yi a ciki da wajen Najeriya ita ce: “Ta yaya za a soke zaben da aka riga aka gudanar?”
Kafin ka ce kwabo, mamaki ya rikide, jama’a suka fusata. Mun ta ba da rahotannin yadda dubban mutane suke fita kan tituna suna zanga-zanga domin nuna rashin amincewarsu. Kungiyoyin fararen hula, dalibai, kungiyoyin kwadago, masu fafutukar dimokradiyya, lauyoyi, ’yan jarida da talakawa, duk suka yi Allah wadai da soke zaben.
A yanzu da nake karanta kundi na, sai na karanto cewa wancan fushin ya hada mutanen Najeriya ba tare da la’akari da bambancin kabila ko addini ba.
Ba shakka, Najeriya ta fada cikin rudani da rashin tabbas. Babu wanda ya san abin da zai biyo baya. A shirye-shiryen BBC Hausa, mun ta yin sharhi tare da yin tambayoyi kamar: Shin sojoji za su janye soke zaben? Shin za a sake gudanar da wani zabe? Shin za a ayyana Abiola a matsayin shugaban kasa? Ko kuwa Janar Ibrahim Babangida zai ci gaba da mulki har sai illa masha Allahu? Kusan kowace rana akan tashi da wata sanarwa ko kuma jita-jita.
Ana cikin haka, zanga-zanga ta barke a sassa daban-daban na kasar, musamman a Kudu maso Yamma. Mun ta ba da rahotanni kan manyan tarurrukan nuna adawa, yajin aiki, laccoci, zanga-zangar dalibai da kuma matakan da kungiyoyin kwadago suka dauka.
Jama’a kuwa suka ci gaba da bijirewa. A wasu birane an rufe hanyoyi da kasuwanni, yayin da wasu kamfanoni suka dakatar da ayyukansu. A hankali, harkar tafiyar da Najeriya ta fara sarkakewa.
Kwatsam sai aka fara kama mutane, ana tsare su ba tare da an yi musu shari’a ba. Mun yi labaran kama masu rajin dimokradiyya, shugabannin kwadago, shugabannin dalibai, ’yan siyasa da ma ’yan jarida. Mu kuwa, duk da cewa muna London, mun kwana da sanin cewa a kowane lokaci ana iya gayyatar masu aiko mana da rahotannin da ke zaune a Najeriya.
A gare ni da kaina, wannan lokaci ya zama wani babban juyin juya hali a rayuwata ta aikin jarida. BBC ta zama daya daga cikin manyan kafafen da ’yan Najeriya suka dogara da su wajen bibiyar abubuwan da ke faruwa. Duk wata sanarwa daga Abuja kusan nan take muke ba da rahotonta. Haka ma duk wani martani daga gwamnatocin Birtaniya da Amurka, kungiyar Commonwealth da sauran kasashen duniya. Sannu na fara kallon kai na a matsayin wata wadda ke da wani babban nauyi akai na.
Matsin lamba ya ci gaba da karuwa. Bayan makonni ana zanga-zanga tare da matsanancin suka daga kasashen waje, sai Janar Babangida ya sanar a ranar 26 ga Agustan 1993 cewa zai “koma gefe” (stepping aside).
Amma maimakon ya mika mulki ga wanda mutane da dama suka dauka shi ya lashe zaben, wato Chief Abiola, sai ya kafa Gwamnatin Rikon Kwarya karkashin jagorancin Chief Ernest Shonekan.
Sai dai ’yan Najeriya kalilan ne suka yi imanin cewa rikicin siyasar Najeriya ya kare a nan.
#jamilahtangaza #June12 #nigeriademocracy
