Hoton Marigari Muhammadu Buhari da Matarsa Ta Farko Da ‘Ya’yansa..
Your message has been sent
An dauki Hoton ne a lokacin yana tare da marigayiyar matarsa Safinatu da Yayansu; Fatima, Hadiza da Zulaihat a gidan gwamnati, a fadar mulki ta Dodan Barrack legas.
Tsohon shugaban kasa marigayi Muhammadu Buhari yayi Aure kafin matarsa da tayi masa takaba Aisha Buhari. Buhari tun yana matashin soja ya auri Safinatu a watan Disamba 1971, jim kadan bayan kammala karatunta na jami’a, kuma sun haifi ‘ya’ya biyar tare, Fatima, Hadiza, Zulaihat, Safinatu da kuma marigayi Musa.
An ce Buhari ya san Safinatu tun tana da shekara 14 kafin aurensu. Matar Buhari ta farko Safinatu ta kasance uwargidan shugaban kasar Najeriya a lokacin da yake shugaban kasa.
An haifi Safinatu Buhari a garin Jos na Jihar Filato a ranar 11 ga Disamba, 1952, Ya’ce ga Alhaji Yusufu Mani da Hajiya Hadizatu Mani wacce ta fito daga karamar hukumar Mani a jihar Katsina kuma ‘yar kabilar Fulani ce ta Arewacin Najeriya.
Lokacin da Musa ‘Yar’Adua, kwamishinan al’amuran Legas a lokacin, ya nada mahaifinta a matsayin sakatare na musamman iyayenta sun koma jihar Legas.
Safinatu Buhari ta yi makarantar firamare da ke Tudun Wada Jos.
A shekarar 1971 ta yi karatu a Kwalejin horas da malamai ta mata ta Katsina inda ta samu shaidar kammala karatun digiri na biyu.
Ta yi karatun Islamiyya kuma tana iya rubutu da Ingilishi da Larabci. Lokacin da Safinatu Buhari tana raye, ta kasance malamar makaranta.
Safinatu Buhari ta hadu da Muhammadu Buhari tana da shekaru 14, kuma sun yi aure tana da shekaru 18 a duniya a shekarar 1971.
Safinatu Buhari ta koma Kaduna da ‘ya’yanta bayan da Ibrahim Babangida ya hambarar da gwamnatin Muhammadu Buhari.
A Shekarar 1988, sun rabu da mijinta Nata
Mutuwa
Safinatu Buhari ta rasu ne a ranar 14 ga watan Junairu, 2006, tana da shekaru 53 a duniya, sakamakon kamuwa da ciwon suga.
