Ko za a iya dakatar da Shari’ar Musulunci a Arewacin Najeriya?
A ranar Talata, 24 ga watan Fabrairu ne majalisar wakilan Amurka ta miƙa rahoton binciken da ta ce ta yi kan zargin muzguna wa Kiristoci a Najeriya, bayan watanni lamarin na tayar da ƙura.
Ɗanmajalisar wakilan Amurka, Riley M. Moore ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar, wadda ta ƙunshi cikakken bayanin kan binciken da hanyoyin da suka bi, da abubuwan da suka gano da ma shawarwari.
Bayan ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da ke buƙatar sa ido da Trump ya yi ne, sai ya kafa kwamitin majalisar domin binciken matsalar a ranar 31 ga watan Oktoban 2025, sannan ya buƙaci Moore da shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar Amurka Tom Cole su jagoranci kwamitin.
Sai dai babban abin da ya fi jan hankali shi ne batun soke shari’ar Musulunci da dokar kisa kan ɓatanci, daga cikin matakai aƙalla shida da majalisar ta buƙaci Trump ya ɗauka.
