Yadda kan iyakar Najeriya da Nijar da Benin ta zama cibiyar ƴanbindiga’
Wani sabon binciken ƙungiyar da ke kula da alƙaluman wuraren da ak gudanar da rikice-rikici ta ACLED ya nuna cewa kan iayakar Najeriya da Benin da kuma Jamahuriyar Nijar na neman zama wata sabuwar cibiyar rikice-rikice a 2025.
Cikin wani sabon rahoto da ƙungiyar ta fitar a ranar Alhamis, ta ce an samu gagarumar ƙaruwar hare-hare a yankin cikin shekarar da ta gabata.
Ko a cikin makon nan ma sau biyu Lakurawa suna ƙaddamar da hare-hare a jihar Kebbi tare da kashe gomman mutane.
ACLED ta ce rikice-rikicen sun shafi ƙungiyoyin JNIM mai biyayya ga ƙungiyar Al-qaeda da EIS mai biyayya ga ISIS, waɗanda suke da alhakin kashi 86 na ƙaruwar hare-haren idan aka aka kwantata da 2024.
”Haka ma an samu ƙaruwar kashe-kashe da kashi 262 cikin 100”, in ji ACLED.
Daga ina ƙungiyoyin suka fito?
Ƙungiyar JNIM da EIS – waɗanda suka jima suna ƙaddamar da hare-hare a ƙasashen yankin Sahel, irin su Mali da Burkina Faso da Nijar – a yanzu sun fara bazuwa zuwa ƙasashen Yammacin Afirka da ke gaɓar teku.
ACLED ta ce an samu ƙaruwar hare-hare a garuruwan Alibori and Borgou da ke kudancin Benin, da yankin Dosso a Jamhuriyar Nijar, da kuma jihohin Kebbi da Sokoto da Neja da Kwara a Najeriya.
Munanan hare-haren masu ikirarin jihadi daga Nijar da Burkina Fasso suka kai wa sojoji a shekarar da ta gabata ya sanya shekarar zama ”shekarar da aka fi samun kashe-kashe” a Benin, kamar yadda rahoton binciken ƙungiyar ya nuna
